Nisaus Sunnah Bauchi
Would you like to react to this message? Create an account in a few clicks or log in to continue.

Go down
Amina
Amina
Posts : 7
Join date : 2022-11-28
Age : 21
Location : Kaduna

ABUBUWAN DA YAKAMATA KA RIKA YIWA MATARKA WANDA ZASU WANZAR DA ZAMAN LAFIYA A TSAKANINKU Empty ABUBUWAN DA YAKAMATA KA RIKA YIWA MATARKA WANDA ZASU WANZAR DA ZAMAN LAFIYA A TSAKANINKU

Tue Nov 29, 2022 11:18 pm


1-Idan tayi fushi jawota ajikinka ka rarrasheta.

2-Idan kaga tayi shiru tambayeta mike damunta.

3-Idan tayi kwalliya ka yabawa kwalliyarta.

4-Idan tayi girki kaci kana santi koda baiyi yadda kake so ba.

5-Idan zata matsa daga kusa dakai riqeta kace baka yadda ba.

6-Idan kaga tana kuka rungumeta ka share hawayen.

7-Idan kaga tana kishinka karka kyareta.

8-Idan zaka fita daga gida ka sumbaceta.

9-Kada kalmar ina sonki da kaunarki ta yanke daga bakinka koda ka manta idan kafita kakirata ka gayamata

10-Idan tayi kuskure ka fahimtar da ita.

11 Idan taji rauni kanuna damuwarka matuka.

12 Idan zatayi aikin gida kataya ta.

13 Idan kuna zaune kuna fira ka rika Koda kyawunta.

14 Idan tamaka laifi kamata uzuri sbd rauninta.

15 Idan ta kyautata maka kagode kuma inda hali kamata tukuici.

16 Idan batada lafiya kabata cikakkiyar kulawa har t warke.

17 Idan tana bukatarka a kusa da ita kabata lokaci.

18 Idan kana mata fada kada kayimata agaban ya'yanta.

19 Idan zakayi shawara kayi da ita.

20 Idan kayi tafiya zaka dawo kagayamata kada kamata bazata.

Tabbas idan kana haka zaku zauna lafiya Insha Allahu
Back to top
Permissions in this forum:
You cannot reply to topics in this forum